Gwamna Lawan ya jaddada aniyar magance ƙarancin ruwa a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Dauda Lawal, a ranar Laraba, ya karɓi rahoton wucin gadi daga kwamitin ba da shawara kan farfaɗo da ruwan sha na jihar Zamfara, yana mai jaddada ƙudirin gwamnatinsa na samar wa babban birnin jihar da sauran ƙananan hukumomin jihar da tsaftataccen ruwamai ɗorewa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Gwamna Lawal ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake karvar rahoton a zauren majalisar da ke gidan gwamnati da ke Gusau.

Gwamnan ya yaba wa tawagar bisa hidimar da suke yi wa jihar da kuma bayar da gudunmawar kason su wajen ciyar da manufar gwamnati ta magance matsalar ƙarancin ruwan sha a faɗin jihar Zamfara.

“Abin farin ciki ne a gare mu da muka samu wannan rahoton na wucin gadi, la’akari da cewa jiharmu na fuskantar matsalar ƙarancin ruwa.

Wannan shi ne ginshiƙan ƙudirinmu na rage raɗaɗin da jama’a ke ciki, kuma ba shakka za a samar musu da ruwan sha.

“Na yi alqawurra a lokacin yaƙin neman zaɓe wanda ya haɗa da magance matsalar rashin ruwa. Ina so in tabbatar wa al’ummar Zamfara cewa gwamnatina za ta yi duk mai yiwuwa don magance wannan matsala.

“Na yi imani da wannan kwamiti, za mu isa can, in Sha Allahu. Za mu shiga cikin rahoton kuma mu yi nazari sosai.

“Za mu yi la’akari da shawarwarin da ke ciki kuma mu yi masu buƙata don magance matsalar da ta daɗe.

“Bugu da ƙari kuma, ina mai farin cikin ganin kwamitin zai faɗaɗa ayyukansa zuwa sauran ƙananan hukumomin, wanda zai samarwa ɗaukacin al’ummar Zamfara ruwan sha.

“Ina so in gode wa ’yan kwamitin da suka yi wannan gagarumin aiki, jajircewar ku abin a yaba ne.”

Tun da farko shugaban kwamitin Engr. Bawa Sani Dauran ya bayyana dalla-dalla yadda kwamitin ba da shawara kan farfaɗo da ruwa ya gudanar da aikin.