Gwamna Makinde ya tsallake masu naɗin sarki ya naɗa Owode sabon Alaafin na Oyo

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Juma’ar da ta gabata, 10 ga Janairu, 2025, Gwamnatin jihar Oyo ta sanar da Prince Akeem Owode a matsayin sabon Alaafin na Oyo.

Gwamnatin jihar ta ce, naɗin zai fara aiki ne nan take.

Sa’o’i bayan sanarwar, wani faifan sauti ya bazu.

A cikin faifan sautin, Awise Agbaye (Babban mai duba al’amuran masarautar), Farfesa Wande Abimbola, ya yi magana game da yanayin da ya shafi naɗin Prince Owode a matsayin Alaafin.

Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife, ya ce biyo bayan damɓarwar da ta biyo bayan naɗin wani Iku Baba Yeye na Oyo, Gwamna Seyi Makinde ne ya tuntuɓe shi ya yi amfani da duban Ifa don zaɓar wani sabon Alaafin. Ya ƙara da cewa, ya yi tattaki daga sansaninsa na Amurka zuwa Oyo, kuma ya shafe kwanaki 10 a kan tabarma, yana tambayar Ifa game da duk sarakunan da suka cancanta.

Ifa, ya ƙara da cewa, ya ɗauko Owode da rahoto mai shafi 21, matar Oyibo ta Awise ta haɗa tare da aika wa gwamna.