Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Bayan shekaru goma ‘yan bindiga na kashe dubban jama’a, tare da karɓar biliyoyin kuɗaɗen fansar waɗanda ake garkuwa da su, Jihar Zamfara ta kafa wata sabuwar Hukumar Tsaron Jama’a, mai suna Community Protection Guard (CPG).
Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana sanarwar kafa hukumar tare da fara yi wa matasan da aka fara ɗauka atisayen ba su horon tunkarar gagarimin aikin daƙile hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.
Sanarwar dai ta fito ne daga bakin Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Jamilu Birnin-Magaji, a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Sanarwar ta ce sabbin jami’an tsaron na sa-kai masu lasisi za su riƙa bayar da gudummawa ce ga jami’an tsaron tarayya, kamar sojoji, ‘yan sanda, NSCDC da sauransu, domin a kakkaɓe matsalar tsaron da ta yi rugu-rugu da yankunan karkakar jihar.
A wurin buɗe ranar farkon fara bayar da horon, Matawalle ya ce wannan gwamnati ta ƙudiri magance matsalar tsaro ta hanyar yi wa matsalar ɗaukar ɗaki cancak, ba wai a riƙa yi wa matsalar kwasar karan mahaukaciya ba.
“Gwamna ya ce gwamnatinsa ta bijiro da sabbin hanyoyin tunkarar matsalar tsaro ka’in-da-na’in a jihar.
“Daga cikin sabbin matakan da aka ɗauka har da kafa Hukumar Tsaron Jama’a a kowace masarauta, daga masarautun jihar su 19.
Gwamna Matawalle ya hori sabbin ma’aikatan samar da tsaron da maida hankali sosai kan ƙalubalen da ke gabansu, wanda gwamnan ya shaida masu cewa babba ne kuma mai wahala.
“A matsayin ku na jami’an tsaro tilas a same ku da kishi. Sunayen ku za su kasance a matsayin waɗanda tarihi ba zai taɓa shafe gagarimar gudummawar da zu bayar ba. Sannan kuma kishin ku da kuma tsantsar ƙaunarku ta ganin an samu wanzuwar zaman lafiya.
“Babu waɗanda za su iya sadaukar da kansu su tunkari wannan gagarimin tashin hankali, sai mai tsananin kishi,” inji Matawalle.
Daga nan sai ya hore su da su riqa tsayawa tare da yin aiki bisa yadda doka ta tsara masu a lokacin da ake ba su horo.
Ya gargaɗe su da kada su wuce-gona-da-iri, kuma su riqa tunawa ba an kafa su don haddasa tashin hankali cikin al’umma ba ne. An kafa su ne don al’umma su wanzu cikin zaman lafiya.
Sauran waɗanda suka yi jawabai a wurin har da Kwamishinan ‘Yan Sandan Zamfara, Ayuba Elkana, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gidan Zamfara, wato tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mamman Tsafe.