Gwamna Ortom ya sha kaye a yunƙurin zama sanata a hannun tsohon hadiminsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya sha kaye a yunƙurinsa na neman kujerar ɗan majalisar dattawan na mazaɓar Arewa maso Yamma a jihar Benuwai a hannun tsohon mai taimaka masa, Titus Zam na jam’iyyar APC.

Jami’in bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Rufus Shaato, ya bayyana Zam a matsayin wanda ya lashe zaɓen mazaɓar Benuwai na Arewa maao Yamma a ofishin INEC da ke Makurdi.

Shaato ya ce, Zam ya samu ƙuri’u 143,151 da ya lashe zaɓen yayin da Ortom ya samu ƙuri’u 106,882 ya zo na biyu yayin da ɗan takarar jam’iyyar LP, Mark Gbillah ya samu ƙuri’u 51,950.

A halin da ake ciki, sakamakon da aka samu daga rumfunan zaɓe daban-daban, mazaɓu da kuma cibiyoyin tattara ƙananan hukumomi a faɗin majalisar dattawan ya nuna cewa gwamnan ya sha kaye a ƙananan hukumomi shida daga cikin bakwai da ya lashe zaɓen Guma.

Zaɓaɓɓen Sanatan shi ne mai baiwa Ortom shawara na musamman kan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, tun da zamansa gwamna a karon farko.