Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta bada kwangilar gina manyan hanyoyi guda uku a garin Funtuwa da za su ci kuɗi Naira biliyan 20.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a garin Funtuwa a lokacin da ya je ƙaddamar da aikin hanyoyin.
Hanyoyin kamar yadda ya bayyana sun haɗa da hanyar da ta taso daga Jabiri zuwa hanyar Gusau mai tsawon kilomita 5.9 da za a maida zuwa tagwayen hanya.
“Aikin zai ci kuɗi Naira biliyan 12.8 da zaran an kammala nan da watanni 18,” gwamnan ya ce.
Sai kuma shatalen-talen Dutsen Rimi zuwa unguwar Mata kan hanyar Katsina zuwa Funtuwa mai tsawon kilomita 3.9,shima zai zi kudi Naira biliyan 8 da za a kammala nan da shekara ɗaya a cewarsa.
“Haka kuma hanyar da ta taso daga Jabiri zuwa Dutsen Rimi da za a gyara, mai tsawon kilomita 1.2 dai shi ma zai ci kuɗi naira 637 da za a kammala aikin cikin watanni shida,” nji Dikko Raɗɗa.
Sai gwamnan ya bayyana cewa da zaran an kammala aikin waɗannan hanyoyi za su taimaka wajan haɓaka tattalin arzikin al’ummar garin musamman masu ƙananan sana’o’i da ke sai dai sai de a waɗannan hanyoyi.
Ya kuma ƙara da cewa garin Funtuwa zai koma kamar manyan birane irin su Katsina da zaran an kammala aikin ginin hanyoyin.
Shugaban kamfanin Mother Cat da aka ba kwangilar aikin hanyar Mr Jack El Najak a nasa jawabin ya tabbatar wa gwamna Dikko Raɗɗa cewa za su kammala aikin a cikin lokacin da akai yarjejeniya da kamfanin.
Ya gode wa gwamnatin Dikko Raɗɗa da aka zaɓi kamfaninsu a matsayin waɗanda a ka ba kwangilar aikin.
Daga baya gwamnan ya ƙaddamar da aikin hanyar Kundura- Charanchi zuwa Gauwa a ƙananan hukumomin Charanchi da Kankia mai tsawon kilomita 52.
Akwai kuma hanyar ƙofar Soro zuwa ƙofar guda da aka kammala.