Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da ɗauka da horas da kashi na biyu na jami’an community watch corps domin faɗaɗa ayyukan tsaro a faɗin jihar.
A ranar Alhamis da ta gabata ne ƴan ta’adda suka kashe jami’ansu biyar yayin da kuma suka samu raunuka a ƙaramar hukumar Jibiya.
Da ya ke jawabi a wajen bikin yaye jami’an, Gwamna Dikko Raɗɗa, ya ce jami’an za su taimaka wa sauran jami’an tsaro wajen yaƙi da ta’adanci a faɗin jihar.
Ya ce jami’ai 1,466 gwamnatin jihar ta ɗauka aiki shekarar da ta gabata waɗanda su na cigaba da gudanar da aikin samar da tsaro a yankunan da ake fama da rashin tsaro.
Gwamna Raɗɗa ya sanar da cewa su waɗannan sune kashi na biyu da aka ɗauka, kuma za su yi aiki a ƙananan hukumomi 10 da aka gano akwai matsalar tsaro a cikin su.
“Kananan hukumomin sun haɗa da; Dutsinma, Kurfi, Charanchi, Musawa, Kankia, Malumfashi, Ƙafur, Ɗanja, Funtua da Bakori”, inji Raɗɗa.
Ya jinjina wa jami’an tsaron da aka ɗauka a shekarar da ta wuce bisa rawar gani da suka taka wajen samar da tsaro inda a yanzu an samu zaman lafiya a yawancin wuraren da ƴan bindiga suka yi kaka gida.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar a yankunan da ke fama da rashin tsaro da su taimaka wa jami’an tsaron wajen bada bayanai da zai taimaka wajan gano maɓoyan ƴan ta’adda da ba su bayanan sirri.