Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya gabatar da Kasafin Kuɗi na shekarar 2025 da adadinsa ya kai Naira biliyan 682 a Zauren Majalisar Dokokin jihar.
Da ya ke bayyani dalla-dalla game da ababen da kasafin ya ƙunsa, gwamnan ya sanar da ƙarin kaso 40 ga kasafin wannan shekarar.
“Fannin ilimi ya fi samun kaso mai tsoka na biliyan N95.9, sai harkar Noma da ta samu biliyan N81.8. Haka kuma fannin tsaro da ya sami Naira biliyan 18.9.”
Gwamnan ya bayyana kasafin kuɗin a matsayin kasafi na al’umma inda ya ce gwamnati ba za ta iya wani motsi ba tare da tallafawa na al’umma ba.
A kan haka ne ya kuma tabbatarwa al’ummar jihar cewa za su cigaba da kwatanta gaskiya da adalci wajen bin ƙa’idar yadda tsarin kasafin kuɗin ya tanadar.
Raɗɗa ya yi godiya ga ƙungiyoyin tallafawa na Majilisar ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin sa kai na ƙasa-da-ƙasa bisa irin tallafawa da goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa.
Da ya ke jawabi, Kakakin Majalisar, Rtd Hon. Nasiru Yahaya ya yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa yadda ya bai wa harkar Tsaro da Kiwon lafiya da Noma da kuma raya karkara muhimmanci.
Ya ce haka za su taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar musamman mutanen karkara waɗanda rashin tsaro ya fi shafa.
Kakakin majalisar ya tabbatar wa gwamnan cewa majalisar za ta dubi lamarin kasafin da kai ziyara wuraren aikace-aikacen gwamnati don tantancewa.