Gwamna Raɗɗa ya gargaɗi sakatarorin ilimi su guji canza wurin aiki ga malamai bisa son zuciya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya yi wannan gargaɗin a lokacin da yake ƙaddamar da rabon kayan karatu guda 200.000 da baburan hawa guda 70 da wayoyin hannu guda ashirin ga malaman firamare gami da tallafi na kuɗi ga ɗalibai masu buƙata ta musamman.

Ya bayyana cewa dole sakatarorin ilimin su cire son zuciya,ko wani dalili da ba na aiki ba wajen canzawa malaman firamare wajen aiki.

Ya yi gargaɗin cewa duk sakataren ilimi da aka samu da aikata wannan aiki za a hukunta shi dai dai laifin da ya yi.

Gwamnan yace shi da kanshi zai rinƙa kai ziyarar bazata a makarantun firamare domin gano malaman da ke zuwa aiki a makare da waɗanda basa zuwa aiki.

Dikko Raɗɗa ya ce yana sane da halayen malamai da ɗalibai na rashin zuwa makaranta da masu zuwa a makare.

Ya sanar da matakai da wasu aikace-aikace da gwamnatin sa ta aiwatar kan harkokin bunƙasa ilmi a jihar da suka haɗa da samar da hakan makaranta, rigar makaranta da littafan karatu na ɗaliban makarantun firamare da basu da hali.

Haka Dikko Raɗɗa ya ƙara da cewa ta rabawa makarantun firamare guda 150 a jihar da kuɗi Naira biliyan 4.737 domin gyara gyaran ɗakunan karatu,wajan ba haya da samar da ruwan sha a makarantun.