
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya yi alƙawarin cigaba da tafiyar da gwamnatinsa bisa gaskiya da riƙon amana ga al’ummar jihar.
Gwamnan ya faɗi haka ne a taron da ya yi da shugabannin ƴaƴan jam’iyyar APC daga matakin ƙananan hukumomi 34 da na jiha wanda ya wakana a gidan Gwamnatin jihar.
Dangane da zaɓe mai zuwa na ciyamomi da kansiloli na ƙananan hukumomin jihar, Gwamna Raɗɗa ya umurce su da su wayar da kan al’ummar jihar akan su zaɓi APC.
Ya kuma yi kira da waɗanda suka mallaki katin zaɓe da su yi amfani da shi wajen mayar da shugabannin da suka taka rawar gani wajen cigaban yankunansu.
A nasa jawabin, Mataimakin gwamnan, Farouk Lawal Joɓe, ya bayyana nasarorin da gwamnatinsu ta samu wajen ƙaddamar da ayyuka da dama na cigaban al’umma.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Sani Aliyu Daura ya umurci shugabannin jam’iyyar a matakai daban-daban da su wayar wa mutanensu don su fito gaba ɗaya su zaɓi APC.
Shi ma mataimakin shugaban jam’iyyar, Bala Abu Musawa ya ce taron an yi shine don nuna kyakkyawan dangantaka da ke akwai tsakanin shugabanni da sauran ƴaƴan jam’iyyar a faɗin jihar.