Gwamna Raɗɗa ya yi naɗe-naɗen farko

Daga UMAR GARBA a Katsina

Sabon gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Raɗɗa ya yi sabbin naɗe-naɗe da suka haɗa da Sakaran Gwamnati, Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Jihar, Daraktan Yaɗa Labarai da dai sauransu.

Naɗin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar.

A wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Raɗɗa ya naɗa Ahmed Musa Ɗangiwa a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar, yayin da Alh. Jabiru Tsauri ya zama Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Barr. Muhtar Aliyu Saulawa shi ne mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, sai Alh. Abdullahi Aliyu Turaji a matsayin Babban Sakataren Ofishin Gwamna.

Sauran su ne, Malam Maiwada Ɗan Malam, Babban Daraktan Yaɗa Labarai, Ibrahim Kaula Mohammed, Babban Sakataren Yaɗa Labarai, Malam Miqdad Isah a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a kan kafafen sadarwa na zamani (Digital Media) da Abubakar Badaru Jikamshi wanda ya zama Babban mataimaki na Musamman (Print and Electronic Media).

Kazalika, Gwamnan ya naɗa Alh. Bishir Maikano a matsayin Babban Mataimaki na Musamman na Tsare-tsare (Protocol).

Sai kuma Alh. Hassan Ibrahim Ɗanhaire a matsayin Babban mataimaki na musamman ta fanni aikace-aikace na ofishin Mataimakin Gwamna da kuma Ahmed Rabiu a matsayin mai ɗaukar hoto na gwamna.

Gwamna Raɗɗa ya taya waɗanda naɗin ya shafa murna, ya kuma buƙace su a kan su haɗa kai da shi wajen ganin an dawo da martabar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *