Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa a ranar Talata da dare ya bi sahun jami’an tsaro daban-daban na jihar domin kai samame mavoyar ‘yan ta’addan da ke ta’addancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin birnin Katsina.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na CPS, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar ga Gwamnan Katsina, ya ce Raɗɗa da kansa ya jagoranci jami’an tsaro suka kai samame maɓoyar ‘yan ta’addan, a daren ranar Talata da misalin ƙarfe 10 zuwa 11:30 na dare.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, maboyar da Gwamnan da tawagarsa ta jami’an tsaro suka kai samame sun haɗa da Sabuwar Unguwa, Sharar Pipe, Dan Hako, Filin Polo, Ƙofar Guga da Tudun Matawalle.
Sai dai Kaula bai bayyana ko an kama wani ba a harin da aka kai cikin dare.
‘Yan ta’addan, a ‘yan watannin nan, sun addabi mazauna yankunan da aka ambata da kuma sauran sassan birnin Katsina.
‘Yan ta’addan sun ƙware wajen ƙwace wayoyi da kuma ƙwacen kadarorin mazauna sassan birnin Katsina.
Yayin samamen da suka kai da dare, Gwamna Raɗɗa, a cikin alƙawarinsa na kawar da masu aikata miyagun laifuka a jihar, ya sake yin watsi da umarnin jami’an ‘yan sanda na su magance ‘yan ta’addan da ke kawo cikas ga zaman lafiya a faɗin jihar Katsina.
Kaula ya bayyana cewa, biyo bayan aikin samamen da aka gudanar a daren jiya a gidajen ‘yan ta’addan, Raɗɗa, da sanyin safiyar Laraba ya kira taron gaggawa da jami’an tsaro a jihar kan sake ɓarkewar laifuka a wasu sassan jihar Katsina.
Raɗɗa ya nuna damuwarsa da rashin jin daɗinsa game da ƙalubalen tsaro da ke addabar jihar, inda ya buƙaci shugabannin tsaro da su ƙara qaimi wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.