Gwamna Raɗɗa zai sake fasalta Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta Jihar Katsina

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya shirya sake fasalta Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta jihar domin bunqasa hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga ga jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin wani taron gaggawa da ya kira hukumomin dake samar da kuɗaɗen shiga ga jihar a ranar Larabar nan 21 ga Yuni, 2023 da ya gudana a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Maigirma Gwamna Raɗɗa ya ce babban maƙasudin wannan taro shi ne don ƙara faɗakar da hukumomin dake samar da kuɗaɗen shiga da su kara matsa kaimi wajen gudanar da ayyukansu domin tattalin arzikin jihar Katsina ya bunƙasa kan haka ne.

Gwamnan ya ce akwai buƙatuwar a sake fasalta ayyukan hukumomin dake samar da kuɗaɗen shiga domin su yi aiki yadda ya kamata.

Sai dai kuma Malam Umaru Raɗɗa ya koka kan yadda ake samun ƙarancin bin doka wajen biyan kuɗaɗen haraji da kuma halayyar wasu jami’an tattara kuɗaɗen haraji da ya ce hakan na a sahun gaba wajen taimakawa ake samun nakasu wajen tattara kuɗaɗen shigar.

“Jihar Katsina na buƙatar hanyoyin samar da kudaden shiga, musamman a wannan halin da ake ciki na ana dab da fara biyan basukan da aka ciwo.”

Malam Dikko Umaru Radda ya ce kudirinsa shi ne jihar Katsina ta rika samar da kudaden da za ta biya albashin ma’aikatan jihar ba sai ta jira dauni daga Abuja ba.

Daga ƙarshe, Gwamnan ya buƙaci Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Arch Ahmad Musa Ɗangiwa da ya kafa kwamiti na musamman da zai yi nazari kan yadda ake samun kuɗaɗen shiga a jihar a wasu jihohin dake samun kuɗaɗen da yawa, domin Katsina ta kwaikwaye su.