Gwamna Sule ya ƙaddamar da rigakafin korona a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Nasarawa Engineer Abdullahi Sule, ya ƙaddamar da allurar rigakafin cutar koron inda shi da mataimakinsa, Dr. Emmanuel Akabe, suka soma yin rigakafin na Oxford-AstraZeneca.

Bikin ƙaddamarwar ya gudana ne ranar Talata a fadar gwamnatin jihar da ke Lafia, babban birnin jihar.

Da yake yi wa manema labarai bayani jim kaɗan bayan ya yi allurar, Gwamna Sule ya yi kira ga ‘yan jiharsa, musamman ma waɗanda suka fi fuskantar haɗarin harbuwa da cutar kamar ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da sauransu, da su tabbatar sun yi allurar.

Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen nuna godiyarsa ga Gwamnatin Tarayya da kuma Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da jihar Nasarawa ta samu rukunin farko na rigakafin.

Kazalika, ya yaba wa duka jami’an jihar da suka yi ta kai komo wajen ganin jihar ta yi nasarar samun maganin.

Daga nan, ya yi jan hankali ga talakawansa kan cewa yin allurar ba shi ke nufin baki ɗaya an fi ƙarfin kamuwa da cutar ba ne, don haka ya ce jama’a su ci gaba da kiyaye ƙa’idojin da aka shimfida na yaƙi da korona zuwa lokacin da a yi rigakafin na biyu.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*