Gwamna Sule ya bada umarnin ladabtar da ɗaliban da suka haifar da zan-zanga a kwalejin Mustapha Agwai I

Daga UMAR M. GOMBE

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bada umarnin a binciko tare da ladabtar da duk wanda aka samu da hannu a rikicin ɗalibai da ya auku kwannan nan a kwalejin fasaha ta Isa Mustapha Agwai I Polytechnic (IMAP) da ke Lafia.

Gwamna Sule ya bada wannan umarnin ne ga shugaban kwlejin, Dr. Justina Anjide Kotso, a Juma’ar da ta gabata, domin tabbatar da an ladabtar da waɗanda suka haifar da rikicin da ya yi sanadiyar lalata kayayyaki da dama a makarantar.

Ya bada umarnin ne bayan da ya kai ziyarar gani da ido a makarantar, tare da bayyana halin da ɗaliban suka nuna a matsayin abin takaici. Yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da zai maida wa jihar hannun agogo baya ba, musamman ma idan aka yi la’akari da irin ƙoƙarin da ya ce gwamnati na yi don inganta fannin ilimin jihar.

Ya ƙara da cewa, ilimi wani ɓangare ne mai muhimmanci ga gwamnatinsa wanda ke ƙoƙarin horas da matasan jihar sana’o’in hannu iri-iri don ƙarfafa musu iya dogaro da kai a rayuwa.

Kazalika, ya yi kira ga ƙungiyar ɗalibai ta makarantar da ta taimaka wa hukumar makarantar wajen zaƙulo waɗanda suka kunna wutar zanga-zangar.

Haka nan, ya gargaɗi ma’aikatan da suka yi amfani da damar da suka samu wajen lalata sashen fasahar sadarwa (ICT), har da ƙirƙiro rasit na bogi saboda son zuciyarsu, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta yarda wannan ba.

Tun farko sa’ilin da yake jawabi, Kwamishinan ‘Yansandan jihar, Mr. Bola Longe, ya ce a tashin farko sun kama wasu ɗalibai su 27 da ke da alaƙa da zanga-zangar, tare da bada tabbacin waɗanda aka samu da hannu dumu-dumu a rikicin kaɗai ne za su fusknci hukunci.