Gwamna Sule ya kawo ƙarshen asusun haɗaka, ya ba wa ƙananan hukumomi ‘yanci

A wani mataki na inganta cin gashin kai na ƙananan hukumomi, Gwamna Sule ya dakatar da asusun haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi.

Wannan sauyi dai na zuwa ne bayan hukuncin kotun ƙolin da ba ƙananan hukumomin ikon cin gashin kan su.

Sanarwar ta fito daga bakin Peter Ahemba, wanda shine babban mataimakin na musamman a Lafia a wata ganawa da manema labarai. Ahemba ya bayyana cewa wannan na nuni da yadda gwamna ke bin doka da oda.

Wannan matakin ya nuna cewa Gwamna Sule ya ɗauki mataki wanda zai inganta al’amuran ƙananan hukumomi, zai basu damar cin gashin kansu da aiwatar da ayyukan ci gaban rayuwa ga mutanen su.