Gwamna Sule ya naɗa Garba Rosha sakataren din-din-din

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A ranar Talata na wannan mako wato 13 ga watan Yunin shekarar 2023 da ake ciki ne Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa wa Honorabul Garba Rosha muƙamin babban sakatare na din-din-din wato Permanent Secretary a turance a majalisar zartaswarsa.

Jim kaɗan bayan babban bikin naɗin nasa wadda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar dake Lafiya babban birnin jihar, wakilin mu ya samu damar ganawa da shi sabon sakataren din-din-din, Honorabul Garba Rosha dangane da naɗin nasa, inda ya fara da miƙa godiyarsa ta musamman ga gwamna Abdullahi Sule game da karamcin.

Ya ce ba shakka ba zai manta da wannan karramawa da gwamnan ya yi masa ba har iya rayuwarsa.

Garba Rosha ya kuma gode wa ɗimbin abokai da ‘yan uwansa daga ciki da wajen jihar musamman al’ummar jihar baki ɗaya waɗanda suka fito ƙwansu da ƙwarƙwata suka taya shi murnar wannan karramawar tun daga gidan gwamnati har gidansa.

Ya ce ba shakka sabon matsayin sakataren din-din-din da Gwamna Sule ya naɗa masa tamkar babban qalubale ne wanda zai yi duka mai yuwa wajen tabbatar bai ba shi da al’ummar jihar kunya ba.

A cewarsa zai yi aiki tuƙuru wajen cimma burin naɗin nasa muƙamin musamman ta hanyar aiwatar da shirye-shirye da manufofin gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule da riƙe amana da yin biyayya don samun bunqasar cigaba a jihar baki ɗaya.

Dangane da jita-jita da wasu da suka nemi muƙaman sakataren dindindin basu samu ba ke yi a yanzu cewa an sa siyasa a sabon naɗin, Honorabul Garba Rosha ya bayyana cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Ya ce gwamnan ya yi la’akari da ƙwarewa da cancanta ne da kuma gudunmawa da shi da wasu da aka naɗa musu muƙaman ke bayarwa da daɗewa wajen cigaban jihar a fannonin rayuwa daban-daban.

Ya kuma yi amfani da damar inda ya shawarci ire-iren masu yaɗa jita-jitar su guji yin haka don a cewarsa Gwamna Sule mutum ne da baruwansa da ra’ayi a naɗe-naɗin muƙaman gwamnatin sa inda ya buƙace su maimakon haka su jira idan lokacin su ya yi gwamnan zai buƙaci nasu gudunmawar.

Idan ba a manta ba a wannan maka da ake ciki ne gwamnan na jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa wannan ƙwararren ma’aikacin gwamnati da ya daɗe yana bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban gwamnatin jihar da ƙasa baki ɗaya wato Honorabul Garba Rosha da wasu mutum 7 a muƙaman sakataren gwamnmatin jihar na dindindin waɗanda a yanzu suna jira a turosu ma’aikatansu daban-daban don kama aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *