Gwamna Bala ya sauke kwamishinoninsa da masu riƙe da muƙaman siyasa

Daga AISHA ASAS

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala A.
Mohammed CON (Ƙauran Bauchi), ya rushe majalisarsa tare da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar.

Sanarwar manema labarai da ta fito ta hannun mai bai wa gwamnan shawara kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mukhtar Gidado, ta nuna Bala ya sauke duka kwamishinoninsa haɗa da wasu masu riƙe da muƙaman siyasa da suka haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar da dukkanin Masu Bai wa Gwamna Shawara (SA) amma ban da wasu mutum huɗu daga ckinsu.

Mutum huɗu da suka tsira da muƙamansu su ne: Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Sha’anin Tsaro da Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Sha’anin Majalisar Tarrayya da ta Jiha da Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Sha’anin Bunƙasa Walwalar Rayuwa da kuma Mai Bai Gwamnan Shawara Kan Sha’anin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a.

Gwamnan ya buƙaci baki ɗaya saukakkun kwamishinonin kowannensu ya miƙa ragamar ma’aikatarsa a hannun Babban Sakataren Ma’aikatar.

Su kuwa Sakataren Gwamnatin Jiha da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnantin Jihar da sauran waɗanda lamarin ya shafa, an buƙace su ne da su miƙa ragamar aiki ga mafi girma daga cikin manyan sakatarori na Fadar Gwamnantin Jihar.

Gwamna Bala Mohammed ya miƙa godiyarsa ga ɗaukacin waɗanda lamarin ya shafa bisa gudunmawar da suka bayar wajen cigaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a rayuwa.