Gwamnan Adamawa ya fifita cigaban ilimi a jiharsa – Sakataren Ƙungiyar Malamai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD
 
Duk da matsaloli da barazanar tsaron da ake fuskanta a arewacin Nijeriya, ba a taɓa daina zuwa makarantu a Jihar Adamawa ba, saboda yadda gwamnan jihar, Ahmad Fintiri, ya fifita harkokin ilimi a jihar. Sakataren ƙungiyar malamai ta ƙasa reshen jihar ta Adamawa, Kwamared  Wakili Kyari ne ya bayyana haka a Kano a yayin taron shekara-shekara na ƙasa da ƙungiyar shugabannin makarantun firamare suka gudanar.

Ya ce Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Fintiri yana bada kulawa sosai ga ci gaban ilimi fiye da gwamnoni da suka gabata, duk da matsalolin da ba za a rasa ba. Domin kafin zuwansa malamai a Adamawa na da matsalar biyan albashi, amma a cewarsa tun da ya kama mulki ba su tava samun tsaiko ba balle rashin biyan albashi.

Ya ce ba wata matsalar su da zai kai masa bai sauraresu akai ba, Kuma kullum ƙofarsa a buɗe take ga malaman makarantu, duk abinda ya taso yana kawo musu ɗauki.

Ya ce gwamnan na Adamawa shine ya soma maida wa’adin ritayar malamai zuwa shekara 40 tun daga shekara ta 2020.

Kwamared Kyari ya yaba da karramawa da ƙungiyar shugabannin makarantun firamare ta ƙasa ta yi wa Rodney S. Nalban, kuma shugaban shiyyar Arewa maso Gabas na ƙungiyar malaman makaranta, sannan sugaban ƙungiyar na jihar Adamawa, wanda an yi hakan ne bisa cancanta kasancewarsa  mutum mai aiki tuƙuru, ƙwazo da riƙon amana.S

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *