Gwamnan Badaru ya miƙa wa sabon Sarkin Dutse sandar mulki

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, ya miƙa sandar mulki ga sabon Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi.

Bikin miƙa sandar ya gudana ne ranar Asabar a Dandalin Aminu Kano da ke Dutse, babban birnin jihar tare da samun ɗimbin mahalarta daga ciki da wajen jihar.

Badaru ya ce sabon Sarkin ya gaji mahaifinsa ne nisa alherin da ya shuka sa’ilin da yake riƙe da masarautar a halin rayuwarsa.

“Muna shawartar ka da ka yi koyi kyawawan ayyukan mahaifinka da kuma tabbatar da shugabanci nagari,” in ji Gwamnan.

Daga nan, Badaru ya yi addu’a wa tsohon Sarkin Dutse, Marigayi Alhaji, Dr. Nuhu Muhammad Sunusi, dangane da shugabanci nagari da ya yi wa masarautar a halin rayuwarsa, tare da fatan Allah Ya ba shi Aljanna.

Kazalika, Gwamnan ya nuna godiyarsa ga Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, zaɓaɓɓen mataimakin Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Sanata Kashim Shatima, tsohon Gwamnan Jigawa, Dr. Sule Lamido, Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Along, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauransu, bisa halartar bikin. of Ringim, Hadejia, Gumel, Kazaure and Zazzau, Kaltingo, Zuru, Bauchi, among others.

A jawabinsa, sabon Sarkin na Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi, ya buƙaci al’umma a yi masa addu’ar samun ikon sauke nauyin da ya rataya a kansa yadda ya kamata.

Haka nan, ya yi alƙawarin zai yi adalci, kuma zai ɗora daga inda mahaifinsa ya tsaya dangane da mulkin masarautar.

Ga ƙarin hotuna na taron bikin:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *