Daga BASHIR ISAH
Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar Bala Abdulkadir Mohammed a matsayin Gwamnan Jihar Bauchi.
Hukumar INEC ce ta bayyana Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da ya gudana ran 18 ga Maris, inda daga bisani babban abokin hamayyarsa na Jam’iyyar APC, AVM Sadique Abubakar (rtd), ya ƙi amicewa da sakamakon zaɓen ya garzaya Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe.
Duk da dai Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen ta yanke hukuncin Mohammed ne halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan Bauchi, amma hakan bai hana Abubakar garazayawa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba.
A zaman da Kotun ta yi a ranar Juma’a, ɗaukacin alƙalan su uku sun yi ittifaki kan cewa ƙarar da Abubakar ya ɗaukaka ba ta da darajar a saurare ta.
Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Chidiebere Nwaoma Uwa, ta ce Abubakar da Jam’iyyarsa ta APC sun gaza gabatar da gamsassun hujjoji kan zargin maguɗin da suka ce an tafka a zaɓen da kuma rashin kiyaye Dokar Zaɓe ta 2022.