Gwamnan Binuwai ya kai bantensa a Kotun Ɗaukaka Ƙara

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta yi watsi da ƙarar da Jam’iyyar PDP a Jihar Binuwai da ɗan takarar gwamnanta, Titus Uba suka shigar.

Masu ƙarar na ƙalubalantar hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta yanke ne a ranar 23 ga Satumba inda ta kori ƙarar tasu kana ta tabbatar da nasarar Hyacinth Alia na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Alƙalan kotun sun ce ƙarar ba ta darajar da za a saurare ta.

Kotun ta ce PDP da ɗan takarar nata sun gaza gabatar da ƙwararan hujjoji don kare zargin amfani da takardun bogin da suke yi wa mataimakin gwamnan APC, Samuel Ode.