Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya gana da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Babban Bankin Nijeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya ziyarci Fadar Shugaban Ƙasa domin tattaunawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Da misalin ƙarfe 2:30 na rana a ranar Talata aka ga motar Shugaba Tinubu ta shiga villa inda masu tsaron fadar suka tarbe shi.

Daga bisani an ga manyan jami’ai sun tarbi Shugaban, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima; Emefiele; Shugaban NNPCL, Mele Kyari; Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa,Tijjani Umar.

Sauran sun haɗa da tsohon Kwamishinan Kuɗi na Jihar Legas, Wale Edun, ɗan Majalisar Wakila, James Faleke da dai sauransu.

A jawabinsa da ya gabatar jim kaɗan bayan rantsar da shi, an jiyo Shugaba Tinubu na cewa zai sake duba dokar canjin kuɗin da tsohuwar gwamnati ta samar wadda CBN ya aiwatar.