
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso na fuskantar ƙorafe-ƙorafe bisa zargin sa da biyan wasu mata Naira miliyan 85 a kowane wata tare da ba su ƙarfin iko fiye da na mataimakansa.
A watan Satumban 2023 ne aka naɗa Cardoso akan shugabancin babban bankin bayan tsige Godwin Emefiele kan ɓarnata dukiya da cin mutuncin aiki.
Rahotonni sun bayyana cewa, Gwamnan bankin ya zo ofiis ne a rana ɗaya da matan yayin da wasu kuma suka ce daga baya suka zo, inda ake cecekuce game da wace alaƙa ke tsakaninsa da su da ta kai ga sun samu damar ɗaukar irin wannan albashi mai tsoka a CBN.
Matan sune Nkiru Balonwu, wadda ita ce ta samar da kamfanin ‘The Africa Soft Power Group’ da kuma wata Daphne Dafinome, wadda babbar akatan ce kuma babbar jami’a a Crowe Dafinone.
Intelregion ta ruwaito cewa daraktoci a CBN sun ce Cardoso ya yi hayar matan ne a matsayin mashawarta ba tare bin tsarin doka ba ko kuma iyakance matakin ayyukansu.
Kamar yadda aka sani, CBN yana da mataimaka gwamna guda huɗu waɗanda sune, Emem Usoro da Muhammad Dattijo da Philip Ikeazor da kuma Bala Bello a ɓangarorin gudanarwa mabanbanta na bankin.
Saidai ma’aikatan bankin suna ayyana matan a matsayin ta biyar da ta bakwai wajen girman daraja a bankin.