Gwamnan Kaduna ya bai wa tsohon ma’aikacin Jaridar Blueprint muƙami

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya naɗa tsohon ma’aikacin Jaridar Blueprint, Samuel Aruwan, a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Birnin Kaduna (KCTA).

Aruwan, wanda ya kasance Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna a baya-bayan nan, tsohon wakilin Jaridar Blueprint ne a jihar kafin daga bisani ya zama shugaban ofishin jaridar na Kaduna.

Masanin aikin jarida ne wanda ke da ƙwarewar aiki na shekaru da dama inda a shekarar 2015 ya koma aiki da gwamnati.

Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya fitar a ranar Talata yaba da ƙwarewar Aruwan a bakin aiki.

Daga nan, Gwamnan ya taya Aruwan murnar samun wannan matsayi, kana ya yi kira a gare shi da ya yi amfani da ƙwarewsrsa wajen bunƙasa birnin Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *