Gwamnan Kano ya dakatar da ma’aikatan da Ganduje ya ɗauka

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da albashin ma’aikata 10,800 da tsohon Gwamnan jihar, Umar Ganduje, ya ɗauka a ƙarshen mulkinsa.

Babban Akanta na jihar Kano, Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai,

Ya ce gwamnan ya dakatar da biyan albashin ne har sai an tantance su domin gane waɗanda suka cancata da kuma ‘yan alfarma.

Abdulkadir Abdulsalam ya kuma ce duk ma’aikatan ƙananan hukumomi da tsohuwar gwamnati ta mayar ma’aikatan jiha a ƙarshen wa’adinta za su ci gaba da karɓar albashinsu na ƙaramar hukuma.

Sai dai kuma ya umarce su da su ci gaba da aiki a ma’aikatun da aka tura su na jiha har zuwa lokacin da za a tantance su domin gano makomarsu.

Akanta Janar ɗin ya kuma yi wa ma’aikata da ‘yan fensho albishirin an daina yanke musu kuɗinsu kamar yadda ya ce ana yi a gwamnatin da ta gabata.

Sannan ya yi kira ga ɗaliban sakandire kusan 60,000 da tsohuwar gwamnati ta gaza biya musu kuɗin jarrabawar NECO har aka rufe rajista cewa wannan gwamnatin ta biya masu, kuma an buɗe shafukan intanet ɗin da za su yi rajista.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *