Gwamnan Kano ya jagoranci buɗe cibiyar wayar da kai ta Musulunci a Garun Malam 

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Gwamnanan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci cibiyar wayar da kai ta  Musulunci wacce gidauniyar Musulunci ta Islamic Enlightenment Foundation of Nigeria (IEFN) ƙarƙashin shugabancin Shugaban Gidauniyar na ƙasa, Malam Abdurrahman Kura ta gina a ƙaramar hukumar Garun Malam da ke Kano wacce aka buɗe cibiyar a ranar Juma’a da ta gabata.

Gwamnan Kano wanda wakilcin Shiekh  Tijjani Sani Auwalu , Kwamishinan al’amuran addini da ke Jihar Kano ya bayyana cewa wannan buɗe cibiya ya yi daida manufar gwamnati na bunƙasa ilimin addini da zamani kuma akwai buƙatar ƙungiyoyi da cibiyoyi da su himmatu wajen ganin an bunƙasa ilimi da sauran abubuwan da zai inganta rayuwar al’umma ta kowanne fanni kuma a cigaba da bada haɗin kai da kawo ayyukan alkairi a duk inda mutum ya samu kansa kuma samun ilimi shi ne babbar arziƙi duniya da lahira don haka gwamnatin Kano ta fifita ilimi akan komai duk da ƙoƙarinda ta ke a fanni Tsaro, Lafiya, Noma da sauransu inda ya yi addu’a fatan zaman lafiya kwanciyar hankali a Kano da Nijeriya.

Tun da farko a nasa jawabin Ustaz Abdurrahman Kura Shugaban Gidauniyar Musulunci ta IEFN ya bayyana cewa wannan cibiya ta ƙunshi masallacin Juma’a da makaranta da makamantansu domin dai yaɗa ilimi ta hanyar koyarwa da sauran wa,azuzzuka domin ilimantar da al,umma na wannan gari da maku santansu a ko wanne lokaci don haka ya yabawa masu taimakawa wannan harka ta yaɗa ilimi a Najeriya da sauran wurare domin cigaban addinin musulinci a duniya baki ɗaya.

Shi kuwa Sarkin Noman Chiromawa Alhaji Yusuf Nadabo Sarkin Noma, a nasa jawabin ɗaya daga cikin manya baƙi addu’a ya yi da fatan alkairi wajen samun zaman lafiya, kwanciyar hankali ƙaruwar arziƙi tsaro a wannnan yanki na mu Kano da ma duniya baki ɗaya, inda kuma ya nuna farin cikin shi da yadda wannan gidauniya ta shiryawa marayu walimar cin abinci a wannan rana inda ya buƙaci ƙungiyoyi da hukumomi da ɗaiɗaikun mutane da su riƙa kulawa da tausaya marayu dai gwargwadon yadda mutum zai iya yi a ko yaushe a ko’ina.

Kaɗan daga cikin mahalarta taron akwai malaman addini irinsu Shiekh Hussaini Rano Shugaban Majalisar Malamai na ƙungiyar Izala na Masarautar Rano wanda ya jagoranci Sallar Juma’a ta farko a wannan masallaci ɗaya daga cikin gina ginan cibiyar Musulunci da ke Garun Malam Kano.

Taron dai ya samu halartar sauran malamai da shugabannin ƙungiyar Izala na ƙananan hukumomin Garun Malam da ƙarmar Hukumar Kura da ke Kano.