Gwamnan Kano ya jagoranci rushe gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci rushe gine-gine da aka yi ba a bisa ƙa’ida ba a filaye mallakar gwamnatin jihar.

Jaridar News Point Nigeria ta tattaro cewar, a ranar Juma’a da daddare kwamitin da Gwamnan ya kafa ya fara rushe gine-ginen da ke cikin Filin Sukuwa na Kano a kan idanun gwamnan yayin da jami’an tsaro ke ba su kariya.

Idan dai za a iya tunawa, sa’ilin da yake jawabi bayan rantsar da shi a ranar Litinin da ta gabata, Abba Gida-Gida ya ba da umarnin hukumomin tsaro su karɓe dukkanin kadarorin gwamnatin da aka sayar a zamanin tsohon Gwamna
Umaru Ganduje.

Daga cikin kadarorin da Gwamnan ke nufi har da filaye mallakar makarantu da wuraren ibada, maƙabartu asibitoci da sauransu waɗanda mallakar gwamnatin jihar ne.

Haka nan, ya ba da sanarwar za a kafa kwamitin bincike nan da wasu ‘yan kwanaki “don tabbatar da duk wani mai hannun cikin badaƙalar ya fuskanci hukunci.”

A wata mai kama da wannan, Gwamna Kabir ya ba da umarnin da a dakatar da duk wani gini da ake yi a Sansanin Alhazan Jihar.

Ya ba da umarnin ne a lokacin da ya ziyarci sansanin domin gane wa idanunsa halin da wurin ke ciki.