Gwamnan Kano ya miƙa sunayen kwamishinoni ga majalisar jihar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane 19 da yake son ya naɗa a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwar jihar.

A ranar Talata ce Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Honorabul Yusuf Falgore, ya karanto jerin sunayen da gwamnan ya aike wa majalisar.

Waɗanda aka zaɓa ɗin dai za su hallara gobe Laraba da ƙarfe 10:00 na safe a gaban majalisar dokokin domin tantancewa.

Ga jerin sunayen kamar haka:

 • Comrade Aminu Abdulsalam
 • Hon. Umar Doguwa
 • Ali Haruna Makoda
 • Hon. Abubakar Labaran Yusuf
 • Hon. Danjuma Mahmoud
 • Hon. Musa Shanono
 • Hon. Abbas Sani Abbas
 • Haj. Aisha Saji
 • Haj. Ladidi Garko
 • Dr. Marwan Ahmad
 • Engr. Muhd Diggol
 • Hon. Adamu Aliyu Kibiya
 • Dr. Yusuf Ƙofar Mata
 • Hon. Hamza Safiyanu
 • Hon. Tajo Usman Zaura
 • Sheikh Tijjani Auwal
 • Hon. Nasiru Sule Garo
 • Hon. Haruna Isa Dederi
 • Hon. Baba Halilu Dantiye

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *