Gwamnan Kano ya naɗa Fauziyya Suleiman a matsayin mai taimaka masa kan harkokin jinƙai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa Fauziyya D. Suleiman a matsayin mai taimaka masa kan harkokin jinƙai da mabuƙata.

Gwamnan ya tabbatar da naɗin Fauziyya ne a ranar Alhamis yayin wani zama da ya yi da jami’an gwamnatinsa a fadar gwamnatin jihar.

Fauziyya D. Suleiman ta yi shura musamman wajen harkokin jinƙai na nema wa mabuƙata da mara sa lafiya tallafi musamman a Arewacin Nijeriya.

Naɗin Fauziyya bai zo wa jama’a da mamaki ba, ganin yadda ayyukan gidauniyarta ta Creative Helping Needy Foundation ba ta tsaya iya Kano ba kaɗai, har ma maƙotan jihohi, inda galibi marasa lafiya da gajiyayyu suke amfana da aikace-aikacenta.