Gwamnan Kano ya naɗa Hisham Habib shugaban Radio Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗin Hisham Habib, shugaban ƙungiyar ‘yan jaridu ta yanar gizo reshen Jihar Kano, a matsayin Manajan Daraktan Gidan Rediyon Kano.

Naɗin wanda ya fara aiki nan take, na cikin wata sanarwa da Hisham ɗin ya fitar, wanda kuma ke riƙe da muƙamin muƙaddashin mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf.

Hisham Habib gogaggen ɗan jarida ne, wanda ya yi digirinsa na farko a fannin Turanci a Jami’ar Bayero Kano, sannan ya yi digiri na biyu a fannin koyon aikin jarida.

Kafin wannan naɗin, Hisham ya yi aiki a matsayin ma’aikaci a Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Kano kuma ya riƙe muƙamin jami’in hulɗa da jama’a a Ma’aikatar Shari’a.

Kazalika, Hisham ya yi aiki a matsayin mai ba da rahoto a fitattun kafafen yaɗa labarai da suka haɗa da jaridar Daily Trust da Daily Independent.

Sannan ya yi aiki a matsayin shugaban Media Cave Limited, wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta, kuma shi ne mawallafi a jaridar News Tunnel.

Ana dai sa ran naɗin Hisham zai ƙara inganta ayyukan Gidan Rediyon Kano da kuma ƙara azama wajen isar da aiki mai inganci ga al’ummar jihar da maƙwamtanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *