Gwamnan Kano ya naɗa Sheikh Daurawa a matsayin Shugaban Hisba

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan muƙamin shugabancin hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Tuni aka miƙa wa Malam Daurawa takardar kama aiki a hukumar ofishin Sakataren Gwamnatin jihar.

A watan Mayun 2019 ne Sheikh Daurawa, tare da wasu jami’an hukumar ta Hisba a wancan lokaci suka ajiye muƙamansu.

Duk da dai babu cikakken bayani kan dalilin ajiye aikin nasa a wancan lokaci, an yi amannar cewa hakan ya faru ne sanadiyyar rashin jituwa da ke tsakaninsa da tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Sheikh Daurawa ya ce ya sake karɓar muƙamin ne kasancewar gwamnatin ta yanzu “Sun nuna min cewa da gaske suke yi, sun nuna min cewa da gaske za su yi aiki.”

Kazalika, ya ce, “Dalilin da ya sa na ajiye aikin a baya shi ne saboda aikin yaƙi yiwuwa daga ƙarshe-ƙarshe.”

Ya ce babban abin da zai mayar da hakali a kai shi ne batun auren zawarawa, kamar yadda gwamnan jihar ya alƙawurta.

“Gwamnan a cikin kamfe ɗinsa ya ce zai aurar da zawarawa da ƴanmata da kuma taimaka wa harkar iyali da marayu da kuma iyayen marayu, waɗanda aka mutu aka bar su da yara. Shi ne abu na farko da za mu sa a gaba,” inji Sheikh Daurawa.

Sannan ya tabbatar da cewa, zai ɗora a kan abubuwa masu kyau da aka yi a Hisbah tare kuma da duba inda za a yi gyara a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *