Gwamnan Kano ya yi sabbin naɗe-naɗe

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi sabbin naɗe-naɗe na waɗanda za su jagoranci wasu hukumomin gwamnatin jihar.

Waɗanda naɗin ya shafa sun haɗa da:

 1. Engr. Ado Ibrahim Umar, Manajin Darakta, Kano Hydo Electricity Development Company (KHEDCO)
 2. Alh. Auwalu Mukhtar Bichi, Manajkn Darakta, Kano State Investment and Properties Limited (KSIP).
 3. Dr. Farouq Kurawa, Manajin Darakta, Kano State Agricultural and Rural Development Authority (KNARDA)
 4. Dr. Tukur Dayyabu Minjibir, Manajin Darakta Kano Agricultural Supply Company (KASCO)
 5. Hon. Hussain Sarki Aliyu Madobi, Manajin Darakta, Sustainable Kano Project (SKP)
 6. Hon. Sadiq Kura Muhammad, Manajin Darakta, Zoological Garden Kano (ZGK)
 7. Engr. Sani Bala, Manajin Darakta, Rural Electricity Board (REB)
 8. Hon. Shamwilu Gezawa, Majajin Darakta, Kano State Rural Water Supply and Sanitation Agency (RUWASA)
 9. Alh. Tukur Bala Sagagi, Manajin Darakta, Kano State Tourism Board
 10. Alh. Yahaya Muhammad Idris Manajin Darakta, Kano State Printing Press
 11. Hon. Adamu Yahaya, Mataimakin Manajin Darakta (DMD), Kano Printing Press
 12. Abba El-mustapha, Sakataren Hukumar Tace Fina-finai ta Kano
 13. Dr. Muhammad S. Khalil, Sakatare, Kano State Watershed, Erosion and Climate Change Management Agency (KN-WECCMA)
 14. Dr. Dahir M. Hashim, Kodineta, Kano State Watershed, Erosion and Climate Change Management Agency (KN-WECCMA)

Sanar da Sakataren Yaɗa labarai ga Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta nuna ana buƙatar waɗanda lamarin ya shafa da su kama aiki ba tare ɓata lokaci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *