Gwamnan Katsina ya naɗa Abdulƙadir Mamman Nasir a matsayin shugaban mai’aikatan gidan gwamnati

Hon. Abdulƙadir M. Nasir

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya naɗa tsohon ɗan Majalisar Wakilai Abdulkadir Mamman Nasir (Andaje)a matsayin shugaban mai’aikatan gidan gwamnatin Jihar Katsina.

Hon. Nasir ya canji Alhaji Ibrahim Jabiru Tsauri ne wanda ya samu muƙamin sabuwar ƙawance don cigaban Afrika ta NEPAD.

Sanarwar ta fito ne daga babban Sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Muhammad Kaula a wata takarda.

Hon. Nasir ya samu takardar shaidar kammala karatun digirinsa ne a Jami’ar Bayero ta Kano kuma ya taɓa rike Hukumar raya Ruwa ta jihar Katsina.

Sauran mukaman da Gwamna Raɗɗa ya naɗa akwai; Malik Anas a matsayin Kwamishina wanda an aika wa majalisar dokoki domin amincewa da buƙatar hakan.

Sai Mustapha Bala Batsari da ya samu muƙamin mai bai wa gwamna shawara kan bunƙasa kasuwanci da Nasiru Ahmad shima mashawarcin gwamna kan raya Karkara.

Sauran sun haɗa da Hajiya Bilkisu Suleiman matsayin mai ba gwamna shawara kan harkokin Banki da Kuɗi, sai Abubakar Ahmad Tsanni a matsayin mashawarcin gwamna kan matasa, sai Dakta Mustapha Shehu, shugaban hukumar cigaban jihar Katsina (KSDMB).