Gwamnan Kogi ya yi barazanar kama masu ƙin karɓar tsoffin kuɗi a jiharsa

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya yi barazanar kamawa da hukunta masu ƙin karɓar tsoffin kuɗi a jiharsa.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Labarai da Sadarwa na Jihar, Mr Kingsley Fanwo, ya fitar a Lakwaja babban birnin jihar.

A ranar Larabar da ta gabata Koton Ƙoli ta yanke hukuncin ci gaba da a,mfani da tsoffin takardun kuɗi na N1000, N500 da N200 har zuwa Disamban 2023.

Da wannan Gwamnan Yahaya ya ce ba daidai ba ne ƙin karvar tsoffin kuɗin duk da Kotun Ƙoli ta ba da damar haka.

“Wannan gwamnatin ba za ta naɗe hannu ta zuba ido tana kallon wasu mutane da ‘yan kasuwa na ƙin karɓar tsoffin kuɗin ba da duk hukuncin kotu.

“A gare mu, ƙin karɓar tsoffin kuɗin rashin biyayya ne ga hukuncin Kotun Ƙoli wanda ba za mu yarda da hakan ba.

“Duk wanda ya ƙi karɓar tsoffin kuɗin a kai rahotonsa ga jami’an tsaro da hukumomin gwamnati don a kama shi a kuma hukunta shi.

“Haka nan, za a rufe bankunan da ke ƙin karɓar tsoffin kuɗi saboda Gwamnatin Jihar ba za ta bai wa bankunan da ke saɓa umarnin kotu wurin zama a jihar ba,” in ji Bello.