Gwamnan Legas ya rushe majalisarsa kwana kaɗan kafin ƙarewar mulkinsa

*Ya umarci su bayyana kdarorinsu

Gwamnan Jihar Legas, Bababjide Sanwo-Olu, ya ba da umarnin rushe majalisarsa haɗi da dukkan hadimansa daga ranar 26 ga Mayu, 2023.

A ranar Laraba Sanwo-Olu ya bayyana hakan cikin sanarwar da Shugaban Ma’aikatan Jihar, Hakeem Muri-Okunola, ya sanya wa hannu.

Sanarwar mai lamba 046 da kuma taken “Ƙarshen Wa’adin Masu Riƙe da Muƙaman Sisaya,” ta nuna Gwamnan ya umarci waɗanda lamarin ya shafa da su bayyana kadarorinsu yayin miƙa ofisoshinsu.

Ya ce, bayyana kadara lamari ne da ya yi daidai da dokar ƙasa.

Sanwo-Olu ya ƙara da cewa, waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da kwamishinoni, masu ba shi shawara na musamma da sauran hadimansa.

Haka nan, ya umarce su da su shirya bayanai kan yadda suka gudanar da harkokinsu sannan su maida dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *