Gwamnan Ondon ya tafi jinya a ƙetare

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya fara hutun jinya na kwana 21 a ƙetare.

Akeredolu ya miƙa wa mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, ragamar mulkin jihar ya zuwa lokacin da zai dawo daga jinyar tasa.

A cikin wasiƙar da ya aika wa Majalisar Dokokin jihar, Akeredolu ya bayyana cewa, Aiyedatiwa zai yi riƙon ƙwarya game da shugabancin jihar har zuwa lokacin da zai dawo.

Kakakin Majalisar Jihar, Olamide Oladiji, ya ce wasiƙar ta nuna ya zuwa 6 ga watan Yuli, 2023 Akeredolu zai koma bakin aiki.

A cewar Mr Oladiji, “Hutun wanda ya fara aiki daga 7 ga Yuni, zai tiƙe ne a ranar 6 ga Yuli, 2023 sakamakon hutun aiki da aka yi na Ranar Dimokuraɗiyya (June 12), da kuma na Idil Kabir da za a yi (28 da 29 ga Yuni, 2023).