Gwamnan Ribas ya rantsar da kwamitin riƙon ƙwarya ga ƙananan hukumomin Jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya naɗa kwamitin riƙon ƙwarya ga dukkan ƙananan hukumomin Jihar guda 23 sakamakon rikicin zaɓe dake gudana a faɗin Jihar.

An gudanar da taron rantsarwar ne a ranar Laraba a fadar gwamnatin Jihar dake Fatakwal, babban birnin Jihar, domin kawo ƙarshen tashin-tashina a sassa daban-daban na Jihar.

Gidan talabijin na ‘channels’, ya ruwaito cewa, sai da gwamnan ya miƙa sunayen mutanen ga Majalisar dokokin Jihar domin tantancewa wanda bayan haka ne suka amince da hukuncin gwamnan.

Haka nan, naɗin ƴan riƙon ƙwaryar ya faru ne sakamakon miƙa ƙudurin ƙara wa’adin shugabancin ƙananan hukumomi da mataimakansu da kuma na kansiloli da Majilisar dokokin Jihar ta yi inda gwamnan ya ƙi amsawa bukatar hakan.

Ganin haka ya sa matasa yin zanzanga da kuma tada hayaniya a wurare da dama ciki har da sakatariyar Majalisar.

Haka kuma, wasu daga cikin masu-ruwa-da-tsaki kan batun, sun kai ƙara kotu kan ƙin amincewa da ƙudurin wanda za’a saurari bayanin a ranar 20 ga watan Yuni, 2024.