Gwamnan Sakkwato ya musanta shirin tuɓe Sarkin Musulmi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu ya musanta zargin da ƙungiyar ƴancin musulmin Najeriya (MURIC), ta yi na cewa yana shirin tuɓe Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III daga kujerarsa.

A kwanakin baya ne babban daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola ya tada batun, inda ya ce gwamnati Jihar na shirin korar Sultan Sa’ad Abubakar daga muƙaminsa la’akari da rikicin Masarauta da ke cigaba da aukuwa a Jihar Kano.

Farfesan ya yi gargaɗin cewa, al’ummar musulmi a Najeriya ba za su amince da hukuncin sauke Sarkin ba inda ya ce Sarki Sa’ad ba Sarkin gargajiya ba ne, na al’ummar musulmi ne.

A watannin baya ne gwamna Aliyu ya tube Sarakuna 15 a Jihar daga muƙammansu wanda hakan ya sa MURIC ke hasashen irin haka ka iya faruwa da Sarkin musulmi Sa’ad.

Yayinda mai girma mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ke magana kan rahoton MURIC, ya ce Sarkin, wani ginshiki ne ga al’ummar musulmi da ke buƙatar girmamawa da mutuntawa inda ya gargaɗi gwamnatin Jihar da ta nisanci duk wani abin da zai haifar da cin mutunci ga Sarkin da Fadarsa.

Leave a Reply