Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku, ya amince da Naira biliyan biyu don sayen motocin alfarma ga kansa, mataimakinsa, da matansu kwanaki 18 kafin ya ƙare wa’adin mulkinsa biyu.
Jaridar Premium Times da ake wallafa wa a yanae gizo ta ruwaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda tsoron kada a yi mata zagon ƙasa ta ce, an amince da hakan ne a yayin taron majalisar zartarwa ta Jiha (SEC) da Gwamna Ishaku ya jagoranta.
“Gwamna Darius Ishaku a taronmu na SEC da ya gabata ya buƙaci majalisar ta amince da takardar da ya gabatar na sayen motoci wa kansa da mataimakinsa da matansu kuma cikin gaggawa aka amince da shi ba tare da wata gardama ba,” inji majiyar.
Majiyar ta ce, an tafka muhawara a wajen taron cewa tun lokacin da Darius da mataimakinsa suka karɓi ragamar mulki a shekarar 2015, suna amfani da tsofaffin motocin da suka gada daga magabata, don haka sun cancanci sabbin motocin yayin da su ke shirin sauka daga mulki.
Sanarwar ta bayyana cewa, bibiyar takardar da gwamnan Darius da matarsa suka gabatar za su samu manyan motoci sama da Naira biliyan 1.3 yayin da mataimakinsa da matarsa za su karɓi motocin da darajarsu ta kai Naira miliyan 750.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, bisa shawarar gwamnan zai samu Toyota Land Cruiser SUV guda biyu, rakiyar Toyota Hilux guda biyu da kuma motar amfani yayin da matarsa za ta samu Land Cruiser SUV da motar rakiya.
Haka zalika, mataimakin gwamnan jihar Haruna Manu, zai karvi ƙananan motocin Land Cruiser SUV guda biyu da kuma motar rakiya guda ɗaya yayin da matarsa za ta samu SUV guda ɗaya.
Lokacin da aka tuntuɓi kwamishinan yaca labarai na jihar, Lois Emmanuel, bai musanta ko tabbatar da amincewar ba.