Gwamnan Zamfara ya aika saƙon gaisuwar sabuwar shekara ga al’ummar Musulmi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya aika saƙon fatan alkhairi ga al’ummar Musulmin jihar bayan shiga shekarar Hijira ta fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), 1446.

Gwamnan, ya yi kira ga al’ummar Musulmi a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya da su cigaba da yi wa ƙasa addu’a domin samun zaman lafiya a dukkan sassan da ake fama da matsalolin tsaro.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce sabuwar shekarar Musuluncin lokaci ne na yin nazari ga abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata.

Yau Lahadi ce ranar farko a shekarar 1446, don haka ya ce akwai rawa da kowa zai taka wajen ganin an samu tsaron mai ɗorewa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya ta hanayar yin addu’o’i a gare ta.

Daga ƙarshe, Dauda Lawal ya yi addu’ar samun farin ciki da cigaba da fatan Allah (SWT) Ya albarkaci jihar tare da kare ta daga dukkan fitina ma da ƙasa Nijeriya.