Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinsa na inganta harkar ilimi, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya amince da a ɗauki malamai guda 2,000 aiki a makarantun faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin zaman Majalisar Zartarwa ƙarƙashin jagorancinsa a gidan gwamnatin jihar dake Gusau.
A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamnan ya jaddada shirin ɗaukar malamai aiki a matsayin ɗaya daga cikin alƙawuran da ya yi a lokacin yawon neman zaɓe.
Sanarwar ta bayyana cewa, ilimi shi ne abu na biyu da gwamnatin Dauda Lawal ya mayar da hankali a kai wanda a halin yanzu ya ke fitar da kyawawan sakamako.
A ranar 14 ga watan Nuwamban 2023 ne gwamnan ya sanar da dokar ta-ɓaci a jihar game da harkokin ilimi, inda daga nan ne aka gina makarantu tare da gyare-gyaren wasu da adadinsu ya kai guda 400 a ƙananan hukumomi 14 dake faɗin jihar.
Haka kuma ya samar da kujerun zaman mutum biyu ga ɗalibai sama da 12,000 a makarantun ƙananan hukumomin.
A lokacin da ya ke jawabi, Gwamna Dauda ya ce aikin ɗaukar malaman na ɗaya daga cikin abin da gwamnatinsa za ta yi a shekarar 2025 don bunƙasa harkar ilimi.
Ya ce za a ɗauki malaman ne bisa cancanta don samar da ingantaccen karatu ga ɗalibai da ma kuma ci-gaba a ɓangaren ilimi.
Ya kuma ce hakan wani ɓangare ne a ƙarƙashin shirin AGILE don yin garambawul ga harkar karantarwa tun daga tushe gami da inganta malamai da ɗalibai a makarantun jihar.
Har’ilayau, Gwamna Dauda ya ce za a fara ne da ɗibar malamai 500 a watanni ukun farko na wannan shekarar musamman na ɓangaren darussan Ingilishi, Lissafi, Chemistry, Physics, Biology, ICT da Kasuwanci (Entrepreneurship).