Gwamnan Zamfara ya ba da tallafin N2m ga waɗanda harin ta’addanci ya shafa

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ba da tallafi na kuɗi Naira miliyan biyu ga waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa a ƙauyukan Janbako da Sakkida da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a jihar.

Kakakin Gwamnan jihar, Nuhu Salihu Anka, ya ce gwamnati ta ba da tallafin domin rage wa waɗanda lamarin ya shafa raɗaɗin harin da suka fuskanta kafin gwamnati ta tattara bayanan abin da ya auku.

A cewar Salihu Anka, “Gwamnati ta ba da tallafin Naira miliyan biyu ga ahalin waɗanda harin ya shafa, kuma nan ba da jimawa ba jami’ai za su fara tattara bayanai kan ɓarnar da aka tafka, kana za a samar da tsare-tsaren da za su sanyaya wahalhalun da jama’a ke fuskanta.”

Kazalika, Gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya ba da tabbacin tallafa wa ‘yan uwan waɗanda suka mutu a mummunan harin.

Lawal ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci yankunan da lamarin ya shafa don yi musu ta’aziyya da kuma jajanta musu kan abin da ya faru.

Gwamnan ya yi ziyarar ne bisa wakilcin Mataimakinsa, Malam Mani Mumini.

Haka nan, ya bai wa ƙauyukan tabbacin gwamnati za ta yi mai yiwuwa don hana aukuwar hare-haren ta’addancin a faɗin jihar.