Daga BASHIR ISAH
Gwamna Duada Lawal na Jihar Zamfara, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da tagwayen hanyoyi a hanyar Gusau zuwa Funtua domin bunƙasa cigaban jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Nuhu Salihu, ya fitar ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar.
Gwamna Lawal ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki wa Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Mamuda Mamman, a ofishinsa.
Ya ce hakan ɓangare ne na alƙauran da ya yi wa talakawansa a lokacin neman zaɓe.
Ya ƙara da cewa, mayar da wannan hanyar ta zama tagwaye aiki ne mai muhimmancin da zai bunƙasa harkokin tattalin arziki a jihar.
Haka nan, ya ce a shirye jihar take don yin haɗaka da Gwamnatin Tarayya wajen aiwatar da ayyukan cigaba a faɗin jihar Zamfara.
A nasa ɓangaren, Mamman ya bai wa Gwamnan tabbacin cewar a shirye ma’aikatar take ta haɗa hannu da Gwamnatin Zamfara a fannin gini hanyoyi don samar da cigaba mai ma’ana a jihar.