Gwamnan Zamfara ya dakatar da cire kuɗaɗe ba bisa doka ba a albashin ma’aikata a jihar

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya umarci a gaggauta dakatar da duk wasu rage-rage da ake yi wa albashin ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

Hakan na zuwa ne bayan da ma’aikata suka yi ta gabatar da ƙorafe-ƙorafe game da rage-rage da ake samu daga ofishin biyan albashi na jihar.

Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, Dauda Lawal ya ce ya ɗauki matakin ne don tabbatar da inganci ga ɓangaren kula da albashin ma’aikatan sakamakon haramtattun hanyoyi da ake bi wajen zaftare musu kuɗaɗe.

Gwamnan ya kuma umarci kwamishinan kuɗi da ya dakatar da baki ɗaya tsarin cire kuɗaɗen ma’aikatan ba bisa ƙa’ida ba, kuma ya sanar da duk hukumomin da ke da hannu acikin hakan matakin da ya ɗauka.

Cikin ababen da aka fake da su wajen zaftare albashin nasu ba bisa doka ba akwai; PAYE, Union Dues, NHF, ZAMCHEMA, Water Rate, FMB (Rent to Own), FMB (Home Renovation) da kuma Housing Corp Loan.

Kakakin gwamnan ya ƙara da cewa, gwamnatinsu na ƙoƙari wajen samar da matakai na kula da ci-gaban ma’aikata a jihar, ta hanyar inganta wajen ayyukansu, samar da wajiban kayayyakin aiki da kuma yanayi mai kyau gare su.