Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, na ci gaba da neman haɗin kan rudunar sojoji domin magance matsalar tsaron da jiharsa ke fuskanta.
A ranar Juma’a Gwamna Lawal ya ziyarci Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja inda suka yi tattaunawa ta musamman.
Sanarwar da Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya rattaɓa wa hannu ta ce, ziyarar Lawal ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen yaƙi da matsalolin tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
“Gwamna Lawal ya ziyarci Hedikwatar Tsaron ne musamman don yaba ƙoƙarin sojoji dangane da yaƙi da ‘yan fashin daji a Jihar Zamfara.
“Ya kuma yi ganawar sirri tare da Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, don tattauna muhimman batutuwa game da sha’anin tsaron jihar,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa, Gwamnan ya damu matuƙa da yadda matsalar tsaron ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa a wasu sassan Zamfara don haka akwai buƙatar yin aiki tare da masu ruwa da tsaki a fannin tsaro domin maido da zaman lafiya a faɗin Zamfara.