Gwamnan Zamfara ya yi sabbin naɗe-naɗe na muƙamai 13

Daga BASHIR ISAH

Sabon Gwamnan Jihar Zamfara, Dokta Dauda Lawal Dare, ya yi sabon naɗe-naɗe na mutum 13 a gwamnatinsa.

Wannan shi ne karo na biyu da Gwamnan ke yin naɗi tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki na jami’an da za su yi aiki tare a sabuwar gwamnatin Zamfara.

A karon farko, Gwamnan ya naɗa Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Mukhtar Muhammad Lugga, a matsayin Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Jihar, sai kuma Abubakar Nakwada a matsayin Sakataren Gwamnati.

Ga jerin sunayen waɗannan sabbin naɗe-naɗen ya shafa:

1) Imran Ahmad Rufai
(Personal assistant P.A)

2) Aminu Almajir
(Deputy chief of staff administration)

3) Sulaiman Bala Idris
(SSA New media)

4) Nura Almajir
(SSA Political matters)

5) Zaharadeen Bello Imam
(SSA Protocol matters)

6) Pharm. Abdulmajid Anka
(SSA Governors office)

7) Mustapha Jafaru Kaura
(SSA Media and Public affairs)

8) Faruku Shettiman Rijiya
(SSA Press Affairs)

9) Kabiru Lawal Muhammad
(SSA Domestic affairs)

10) Shamsuddeen Muhammad
(SSA Domestic)

11) Ali Akilu Bungudu
(SSA Economic matters)

12) Mugira Yusuf
(Special assitant on New media)

13) Babangida Bisu
(Special assitant protocol)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *