Gwamnati ba ta da wani hanzari kan rashin samar wa al’umma sauƙin rayuwa

Daga NAFI’U SALISU

Duk wanda yake kishin ƙasarsa da al’umma tare da ci gaban ƙasa, to shakka babu tilas ne ya nuna kishinsa ta hanyar da zai iya yin hakan, ko da kuwa hakan zai zame masa barazana a rayuwa, domin dai ita gaskiya guda ɗaya ce, kuma ko ka faɗe ta ko ka yi shiru, to gaskiya tana nan a mazauninta na gaskiya don ba za ta tava zamowa ƙarya ba.

Na yi rubuce-rubuce da dama a kan halin da ƙasar nan ta samu kanta a jiya da yau, hakazalika, na sha yin maganganu na jan hankali a kan mahukunta wajen kula da rayuwar al’ummar da suke shugabanta, ko da ba za su gani su karanta ba, ko da ba za su kalli abinda na rubuta su yi wani abu a kai don al’umma su samu sauƙi, to ni dai ban yi a banza ba, saboda na yi abinda zan yi ne don sauke nauyi. Ƙila akwai ire-irena da yawa da suke son yin magana kan al’ummaran da suke faruwa na rashin dai-dai a ƙasar nan amma ba su yi magana ba sai a dalilin ganin tawa maganar, ƙila kuma akwai waɗanda suka gani kuma suka karanta a cikin jagororin al’umma, suka yi wani abu na a zo a gani don faranta ran jama’a.

A yau ina son zan yi bayani ne a kan abubuwa guda biyu da ya kamata a ce Gwamnatin Nijeriya ta mai da hankali a kansu fiye da samar wa ‘yan ƙasa wasu abubuwa da su suka fi buƙata ba. Na farko magana ce a kan tsaro (security), sai abu na biyu shi ne walwala/jin daɗi wato (walfare). Waɗannan abubuwa su suka fi komai muhimmanci a halin yanzu ga duk wani ɗan Nijeriya, kuma wannan na cikin kundin tsarin mulkin ƙasa da doka ta tabbatar, yana nan kuma a kundin tsarin mulkin ƙasar nan (1999).

Samar da tsaro wajibi ne a cikin ƙasa, kuma shi ne abinda zai ba wa ‘yan ƙasa damar gudanar da al’amurransu cikin tsari da kwanciyar hankali a ko’ina ba tare da fargaba ko tsoro ba. Idan ƙasa tana da tsaro, babu wanda zai iya ɗaukar makami ya yi ta’addanci ba tare da an hukunta shi ba, sannan duk wata ƙasa ba za ta ji tsoro ko ɗar-ɗar na zuwa ƙasar da ke da tsaro ta zuba hannun jari ba, haka nan a fannin cinikayya ƙasashe da dama za su yi sha’awar ƙulla hulɗar kasuwanci.

Amma yau a irin abubuwan da suke faruwa a Nijeriya na (Insecurity) matsalar rashin tsaro, hakan ya haifar da illar da Nijeriya ke komawa baya, kuma wannan babban abin takaici da kunya ne a duniya, a ce ƙasa kamar Nijeriya da ta fi kowacce ƙasa a nahiyar Africa, take da arziki da ma’adanai a ƙarƙashin ƙasa, da albarkar ƙasar noma da tsirrai, amma an wayi gari kullum muna komawa baya, duk a dalilin rashin tsaro.

Abu na biyu wato (walfare), samar da jin daɗi da walwala a zukatan al’ummar ƙasa daga arzikin ƙasa da dukiyar da ƙasa ke tarawa, duk wannan ana yi a kowacce ƙasa da ake kishin al’umma, baya ga haka ma kuma duk yana daga cikin dokar ƙasa, tilas ta samar wa ‘yan ƙasa (social walfare) domin kawar da talauci da raba ƙasa da aikata miyagun ayyuka. Shi ne a riqa babda wani tallafi na kuɗi ga ‘yan ƙasa (musamman talakawa da naƙasassu masu buƙata ta musamman).

Akwai ƙasashen da suke yin wannan da dama, waɗanda ake ba su tallafin kuɗi, za ka ga mutum mai mace ɗaya da yara biyu ko uku a duk wata ana ba shi Dalar Amurka 2000 ($2,000) wajen Naira miliyan huɗu kenan, to wanda yake da yara sama da haka, ko wasu ‘yan uwa da ke ƙarƙashinsa kuɗin da yake karɓa na tallafi daga Gwamnati ya fi na wancan mai mata ɗaya da yara biyu ko ukun.

Haka nan maras aure, ko gwauro duk ana basu sai dai ƙasa da waɗanda suke da iyali. Amfanin yin hakan shi ne, raba ƙasa da ɓatayi, ko v’ɓatagari da ‘yan tawayen da za su ɗauki makami su ce za su yaqi gwamnati, domin suna samun abinda suke so. Don haka kaga ba ma za su taɓa yin tunanin aikata wani mummunan aiki ba, sannan ba za su bari wani ya aikata ba.

To mu a nan Nijeriya shi kansa rashin tsaron an maida shi kasuwanci, a cikin mutane farar hula da jami’an tsaro akwai marasa kishin ƙasa da son tara abin duniya da suke taimakawa waɗanda suke aikata miyagun ayyuka yin aikin, akwai a cikin sarakuna da gurɓatattun ‘yan siyasa masu mulki da jinin talakawan ƙasa. Haka nan idan gwamnati ta ware abubuwan tallafi da jin ƙai da ya shafi ɓangaren (walfare), sai a karkatar da kayan a haɗa baki da miyagun ‘yan kasuwa a zalunci al’umma.

Babban abin takaici da baƙin ciki shi ne irin yadda al’amura suke ƙara lalacewa suna tavarvarewa (musamman a yankin Arewa), in da har yanzu akwai ƙarancin wayewa da rashin sanin ciwon kai tare da rashin kishin ƙasa. Yankin Arewa ya fi kowanne yanki lalacewa a fannin tsaro, kasuwanci, ilimi, kiwon lafiya, noma da sauransu. Amma kuma mu ‘yan Arewar a haka muke kiran kanmu wayayyu.

‘Yan siyasarmu suna amfani da mu wajen gwara kai, da jin haushin juna, gaba da ƙiyayya amma har yanzu mun kasa gane dare daban rana daban, muna tafiya cikin duhu da sunan haske.

Mawadatanmu da ‘yan kasuwa suna gasa mana gyaɗa a hannu muna godiya da juya bayan hannu muna lashe ƙuna da raɗaɗin azabar da suke gana mana muna cewa zuma muke lasa ƙannenmu da ‘ya’yanmu sun kasa samun ingantaccen ilimi don su yi rayuwa mai kyau, saɓanin haka sai suke ƙarewa a yawon bola da tallace-tallace tare da yin bara a bakin titi.

Iyayenmu mata da ya kamata su samu kyakkyawar kulawar da za su raini ‘ya’ya cikin tarbiyya, amma sai rainon ya koma wasarere saboda ƙunci da uƙubar rayuwa sakamakon matsi da talauci.

Gidajen gyaran halin ƙasarmu Nijeriya ƙara cika suke yi da masu aikata laifi saɓanin su ragu, kullum sai an kai sabbin masu laifi, wasu sun shafe shekaru suna jiran hukunci, laifinsu ma bai taka kara ya karya ba, amma sun shafe shekaru da dama an ajiye su an manta da su.

Tun mutum yana nadamar zuwansa wurin har ta kai ga yana ɗarsa wa zuciyarsa mummunan tunani, da zarar an fito da shi zai aikata babban laifi. Shi kenan daga nan ya zama gawurtaccen ɗan ta’adda, zai koyar da wasu, su kafa ƙungiya su warwatsu ko’ina suna aikata ɓarna.

To wannan ya zama ci gaba ko ci baya? Duk ƙasar da take son ganin al’umma cikin salama, tare da tafiyar al’amura lami-lafiya, to tabbas sai ta kasance mai faranta ran ‘yan ƙasar. Hakan shi zai cire mummunan tunani a zukatan ‘yan ƙasa, ya sa musu kishin ƙasa da qaunar shugabanni, ya sa ‘yan ƙasa tunanin ƙirƙirar abinda zai kawo wa ƙasarsu ci gaba ba ci baya ba.

Amma a rayuwar da muke yi a yanzu a Nijeriya, hatta mai sayar da gyaɗa ‘yar ƙauye da ta fito daga Karkara ta zo birni tallar gyaɗa sai ta yi algus da ha’inci, dalili kuwa shi ne, shugaban ƙasarta azzalumi ne, gwamna da muƙarrabansa azzalumai ne ba ta al’umma suke yi ba.

Ta inda za ka gane hakan shi ne, duk shugaban da zai ƙaƙaba wa al’umma abu wanda ko suna so ko basa su sai ya yi, to wannan ba shugaba adali ba ne, shi shugaba idan zai yi abu sai ya nemi ta bakin jama’ar da yake shugabanta.

Misali mu ɗauki cire tallafin mai, ƙara haraji ga kamfanoni, ƙirƙirar asusu ɗaya (single account), wanda duk wani (transaction) da za ka yi a Banki ana gani kuma ana cire maka kuɗi, sannan ga ƙaramin albashi, ga ƙarin kuɗin haraji da ya wuce misali.

Dukkan waɗannan abubuwan Gwamnati na duba illar da za su haifar kafin ta haɓɓaka su, to amma mu a nan Nijeriya abin ba haka yake ba, face kawai gwamnati na fitar da aiki ne, ko ƙirƙiro aiki don samun wani kaso mai tsoka nata, ba wai don ci gaban al’umma ba.

Idan da ana yi ne don ci gaban al’umma, to da tuni an kawar da matsalar cin hanci da rashawa da tsaro, da an kawo ƙarshen duk wani ta’addanci da ake yi a Nijeriya.

Don haka batun walwalar jama’a da inganta tsaro su tabbata, wannan shi zai tabbatar da ana kishin ɗan ƙasa, amma matuƙar waɗannan abu biyun ba su samu a Nijeriya ba, kuma suka tsaya komai ya daidaita, to babu wani abu da ya shafi jin daɗi ko kwanciyar hankali a wajen ɗan Nijeriya, kuma ayyukan ɓarna za su ci gaba da ƙaruwa, ko da za a ci gaba da ɗaukar sabbin jami’an tsaro ƙasar nan ba za ta gyaru ba har sai an tabbatar da samuwar tsaro da samar da cikakkiyar kulawa ga ‘yan ƙasa.

Mu kalli abinda ke faruwa a jihar Legas, wanda ya dace a ce gwamnoninmu na Arewa ne suka fara yin haka, yanzu gwamnatin jihar Legas ta samar da kasuwa da talakawa za su riƙa zuwa sayen kayan masarufi cikin sauqi, duba da tsadar rayuwa da ake ciki, inda za a rage kaso ashirin da biyar cikin ɗari 25%. Amma su gwamnatocinmu ba a iya jin ƙoƙarinsu sai idan an zo gaɓar da za su yi amfani da ita wajen campaign.

Na faɗa a rubutuna na baya cewa, ita Gwamnati ta san duk yadda za ta yi ‘yan ƙasa su samu sassauci a duk lokacin da aka shiga cikin ƙunci a sanadiyyar karyewar tattalin arziki, ko ma a duk wani hali da ake ciki.

Babu wata ƙasa ko gwamnatin al’umma da za ta ce ba ta san yadda za ta samar wa ‘yan ƙasa abinda zai rage musu raɗaɗin rayuwa ba, haka nan gwamnati ta san abinda idan ta yi shi zai girgiza al’ummar ƙasa, ya jefa su cikin mawuyacin hali da ƙuncin rayuwa, koda a tunani da hangenta za ta yi ne a kan wasu ɓarayin ƙasa.

Misali kamar yadda tsohuwar gwamnatin Buhari ta yi, shi ya san cewa abubuwan da ya ƙirƙira zai jefa al’ummar ƙasa cikin takura da ƙuncin rayuwa, amma haka ya yi bai fasa ba, saboda a tunaninsa zai yi maganin wasu tsirarun mutane da yake ɗauka a matsayin waɗanda suke kawo koma-baya a Nijeriya.

Irin wannan tunanin shi kansa koma-baya ne a wajen duk wani shugaban da zai jagoranci al’umma, a matsayinka na wanda ka samu shugabanci ba baya za ka kalla ba, gaba zaka kalla ka manta da abubuwan da suka wuce ka kawo naka sabbi da za su gina ƙasa da al’ummar ƙasa, amma duk wani shugaban da yake da tunani irin na tsohon shugaban Nijeriya Buhari, to ba zai tava yin abinda zai ciyar da Nijeriya gaba ba sai dai samar da koma-baya.

Mu kalli barazana da vavatu tare da surutan da ƙungiyoyi irin su Amnesty, ECOWAS da CEDEOA suka yi ta yi a kan ƙasar Nijar, yau an wayi gari ECOWAS ta cire takunkumin da suka saka wa Nijar, wutar lantarkin da aka yanke musu an maida, an buɗe iyakar ƙasa-da-ƙasa ta Nijar da Nijeriya, shin a tunaninku duk me ya kawo haka? Siyasa ce kawai ba wani abu ba, amma kar ku ɗauka an yi ne don ‘yan ƙasa.

Kuma ƙasar Nijar ta nuna da gaske ƙasarta take kishi da al’ummar ƙasar, don haka cikin sauƙi gwamnatin qasar ta fito ta nuna manufarta ga ‘yan ƙasa, kuma suka fara gani a aikace zahiri ba a wasan kwaikwayo ba na irin abinda ke faruwa a Nijeriya, don haka suka mara wa shugaban ƙasa Abdurrahman Tchani baya da gwamnatinsa. Inda ba ƙasar da ‘yan ƙasar ne a gabansa ba, to da tun lokacin da ƙungiyar ECOWAS da takwarorinta suke barazanar saka takunkumin yanke hulɗa, da cire wutar lantarki da duk wasu abubuwa daga Nijeriya da wasu ƙasashen, to da tun a lokacin shugaban ƙasar zai ba da haquri a yi yadda ECOWAS da sauran masu son a yi abinda suke so a yi.

To amma sai bai nuna tsoro ko fargaba ba, bai kuma yi nadama a kan juyin mulkin da suka yi ba, sannan ya bayyana dalilan da suka sa su yin shi kansa juyin mulkin. Ba komai ba ne face taɓarɓarewar tsaro, da cin hanci da rashawa da suka fara yaɗuwa a jamhuriyar Nijar.

To mu a Nijeriya bayan rashin tsaro muna da tarin matsaloli waɗanda suke mai da ƙasarmu baya a kullum, amma gwamnatin Nijeriya ba ta su take yi ba. Mun dai ga bayan cire tallafin mai (subsudy), an fara ɗauke wasu manyan abubuwa daga Arewa ana maida su kudu, kuma manyan Arewan ko a jikinsu.

Ɗan majalisa Abdul Ningi ya yi ƙorafin cusa wani kasafin kuɗi ba bisa ƙa’ida ba an dakatar da shi cikin gaggawa ba tare da an saurari cikakken bayanin dalilinsa ba. Shi kansa rashin gaskiya a Nijeriya yana da masu kare shi da bashi goyon baya, wannan shi zai tabbatar da cewa matuƙar za ka yi gaskiya da adalci a shugabanci, to a Nijeriya ba za ka je ko’ina sai idan Allah Ya ba ka taimakonsa.

Mu dai ‘yan Nijeriya ne, kuma muna kishin ƙasarmu tare da fatan ganin al’amura sun daidaita, don ya zama wajibi ni da ku mu ci gaba da gwagwarmaya don nuna kishin qasa ko da ta hanyar rubuce-rubuce ne, ƙila hakan watarana yayi tasiri burinmu ya cika koda bayan babu mu raye a duniya.

Nafiu Salisu
Marubuci/manazarci ya rubuto daga jihar Kano, Nigeria.
Email:[email protected]
[email protected]
0902 984 5489