Gwamnati na shirin kashe tiriliyan N1 don gina masana’antu a ƙananan hukumomi 774

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ƙudirin ƙirƙiro da masana’antar cikin gida guda ɗaya a kowace ƙaramar hukuma daga ƙananan hukumomi 774 da ake da su a ƙasar nan. Gwamnatin ta ce tana sa ran kashe kuɗi naira tiriliyan N1 ne domin cim ma wannan ƙudiri.

Ministan Ayyuka na Musamman, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan yayin ganawarsu da Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Ayyuka na Musamman. Inda ya ce irin wannan masana’anta ta cikin gida za ta maida hankali ne wajen samar da kayayyakin masarufi don amfanin al’ummar yankin da aka kafa masana’antar a cikinta.

Da yake amsa tambayoyin mambobin kwamitin, Ministan ya ce yanzu haka suna kan tattaunawa tare da Shugaban Ƙasa kan batun. Tare da cewa idan Shugaban Ƙasa da Majalisar Zartarwa suka amince da batun, ma’aikatarsa za ta soma aikin gina masana’antu a cikin Yuni mai zuwa.

Haka nan, ya ce akwai wani shiri na daban da ɓangare mai zaman kansa ya yi inda zai kashe kuɗi tiriliyan N19 ga shirin samar da masana’antun a sassan ƙasa a tsakanin shekaru goma, baya ga Naira tiriliyan guda da Gwamnatin Tarayya ta shirya kashewa.

Ministan ya bayyana cewa Naira tiriliyan guda da gwamnati ke sa ran kashewa za ta samo kuɗin ne daga ƙoƙarin ɓangare mai zaman kansa wanda za ta biya kuɗin ruwa na kashi 2 wanda hakan ne ma ya kwaɗaita wa ‘yan kasuwar yanke shawarar shigowa don a yi aikin tare.

Game da ƙalubalen matsalar rashin wutar lantarki da shirin ka iya fuskanta, Ministan ya ce gwamnati ba ta mance da batun lantarki ba yayin da take ci gaba da tsare-tsarenta na samar da masana’antun. Tare da cewa gwamnati za ta haɗa har da amfani da hasken rana wajen samar da lantarkin a wuraren da akwai buƙatar hakan.

A cewar Ministan, “Da muka ce masana’antar cikin gida, muna nufin masana’antu irin waɗanda ke da ƙarfin samar da abubuwa irin su; kayan shayi da lemon kwalba da makamantansu, amma ba samar da siminti ko motoci ba.”

Tun farko sa’ilin da yake jawabi, Shugaban kwamitin, Sanata Abubakar A. Yusuf (APC dagaTaraba ta Tsakiya), ya buƙaci ƙarin haske kan ko Naira tiriliyan guda da gwamnati ta ce za ta kashe, daga aljihun gwamnati kuɗin zai fito ko kuwa a jikin ‘yan kasuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *