Gwamnatin Ƙasar Congo Brazzaville ƙarƙashin jagorancin Shugaba Denis Sassou Nguesso ta ƙaryata yunƙurin juyin mulki a ƙasar.
Ta bayyana haka ne cikin wani saƙo da ta wallafa a Tiwita a ranar Lahadi.
Kafafen yaɗa labarai da dama sun ruwaito ranar Lahadi cewar sojoji ana yunƙurin kifar da gwamnatin ƙasar a yayin da Shugaban Ƙasar yi tafiya.
Saƙon X (Tiwita) da Ministan Sadarwa da Yaɗa Labarai na Ƙasar, Thierry Moungalla, ya wallafa a shafinsa ya ƙaryata haka.
“Gwamanati ta ƙaryata rahoton. Muna sake jaddada wa al’umma zaman lumanar da ke akwai a ƙasar, muna kira ga jama’a kowa ya ci gaba da harkokinsa hankali kwance,” in ji saƙon.
Shugaba Nguesso tsohon soja ne wanda ya soma mulkin ƙasar tun a shekarar 1997.