Gwamnati ta ɗage shirin ƙidaya zuwa Mayu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɗage shirin ƙidayar al’umma da ta shirya farawa 29 ga Maris ya zuwa watan Mayu, 2023.

Ministan Labarai, Lai Mohammed ne ya ba da tabbacin haka jim kaɗan bayan taron Majalisar Zartarwa da ya gudanar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ya ce ɗage shirin ya zama babu makawa sakamakon ɗage zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi da aka yi zuwa 18 ga Maris.

Lai ya ce Majalisar ta amince da bai wa Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, NPC, kuɗi Naira biliyan 2.8 don tanadin kayan aikin da za ta yi amfani da su wajen gudanar da shirin.

Idan za a iya tunawa, a baya Manhaja ta rawaito hukumar NPC na cewa ɗage zaɓen gwamnoni zai shafi shirin ƙidayar da ake shirin gudanarwa.

Wannan shi ne shirin ƙidaya na farko da za a gudanar a ƙasar tun bayan wanda ya gudana shekaru 17 da suka gabata.